Skip to main content

DAN ZARIA A RESTAURANT

Wani shakiyin Bazazzagi ne ya yi dinkinsa babbar riga mai asake akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. Da ka ganshi ka ga mai hannu da shuni. Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna ya kwalawa mai restaurant kira da karfi ya ce “Hado min plate na Naira 2,000 kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3, 000 saboda idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”. Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa ta kawo masa hadin girma. Shinkafa da dankalin turawa da farfesun kayan ciki ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so. Kana ga hadin kwadon kayan lambu da a turance a ke kira da salad Bayan mutumin ya gama cin abinci sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500 kuma ki baiwa kowa na Naira 1, 000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”. Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala. Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar “Allah ya kiyaye ka!” Bayan mutumin ya gama sai ya cewa mai Restaurant “kawo min resit na biya kudina kuma ki kaiwa kowa nasa resit ya biya kudinsa, saboda idan ina biyan kudina ina so naga kowa yana biyan nasa”. Wane hukunci mai restaurant da mutane zasu yi mai?

Comments

Popular posts from this blog

MAZAN ZAMANI

A wannan zamanin da muke ciki in kana neman kwararrun mayaudara wadanda sun kware kuma sun san salo iri-iri na yaudarar 'yan mata sune mazan wannan zamanin da muke ciki.sai yace hana son ta amma cikin zuciyar sa babu komai sai tsabagen yaudara da dabarun yadda zai sami nasara ya tsima ta don neman cin nasara a abin da ya hango kuma shi ya kai shi.shi fa ba auren ta zai yi ba amma saboda ya riga ya kafa mata tarko kuma yayi nasrar kama ta kurunkus, ta faru ta kare.a haka zai cigaba da cin nasara a kan ta daga gaya in ya gama cin moriyar ganga sai ya fasa ya canza sabuwa.ita kuma sai ta zama abar tausayi mai nadama da dana sani, da na sani keya ce.

BEATING THE CHILD

There is a difference between punishment and discipline. Punishment is good because it tells the child that actions have consequences. But punishment must lead to a point where a child can, on his own, choose not to misbehave. That point is called DISCIPLINE. A disciplined child can make the right choices unsupervised. Unfortunately, many times punishment does not lead to discipline because of wrong administration. There are common mistakes parents make when punishing and the end result is negative. Many children even become stubborn. Here are some rules for punishment... 1. Never ever beat a child out of anger. No don't do it. You came back from work and noticed that Bala has broken the centre table due to excessive play. You get so angry that you land Bala a few dirty slaps while screaming at him. WRONG! I know your table is expensive but that child's character is more valuable. Be the parent. Be in control of your emotions. When you react out of anger, you're telli...