Don girman Allah a taimaka a amsa man
tambayata. Allah yaima sakayya da gidan Aljanna
mlm. na kasance daya daga cikin members na wannan page kuma ina bibiyar fatawoyinka. mlm ina
fama da matsalar sanyi (gonorrhoea), wato wani
farin ruwa ke fitowa daga azzakarina shine nake
so mlm ya taimaka man da magani don naji ance
wannan matsalar na hana mutum haihuwa kuma
gashi saura wata ukku bikina, sannan kuma ina
gudun kar in gogama matar da xan aura. na
jarraba wani daga cikin magugunan da kai bayani
ga irin wannan mtslar a baya na garin tafarnuwa,
citta da kustilhindi a cikin zuma duk inna sha sai
zuciyata ta rika yin ciwo. kuma na jarraba wanda
ka bada ga tambaya ta 1458 shima ban dace ba.
mlm a taimaka a amsa man don na dade ina
fama da wannan matsalar kuma abin na damuna.
mlm a boye sunana. na gode.
AMSA
*******
Shi wannan sanyin gaskiya yana da wahalar jin
magani. Domin kuwa wadancan abubuwan da ka
ambata a baya, mutane da yawa sun jarraba
kuma sun samu waraka da yardar Allah.
Amma ga wasu nan ga jarraba:
1. Ka nemi Man Habbatus sauda dan Misra ko
Algeria ko Hemani. Ka gaurayashi da man
Tafarnuwa Original tare da Man Albabunaj.
Sannan ka rika dafa 'danyar chitta (Ginger) da
ruwa kofi guda. idan ya dafu sai ka sanya
wancan Man chokali guda aciki, sannan ka sanya
zuma daidai gwargwado, sannan kasha.
In dai sanyi ne, kowanne iri ne in sha Allahu zaka
samu waraka.
Ka samu Furen Albabunaj (chamomile flower) ka
rika dafa cokali guda kana sha kullum da safe. In
sha Allah Wannan zai wanke maka Qodarka da
mafitsararka, Kuma zai magance maka
Matsalolin ciwon sanyi.
WALLAHU A'ALAM.
Admin Mbello
08030911989 WhatsApp
Karanta Sababbin Kalaman Soyayya Masu Ɗaukar Hankulan Ma'abota Soyayya : ALMARA A SOYAYYA. A duk lokacin da na zauna zuciyata tana rada mini cewa, ranar da aka haifeki ta kasance rana ce da aka yi ruwan sam...
Comments
Post a Comment