Wani shakiyin Bazazzagi ne ya yi dinkinsa babbar riga mai asake akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. Da ka ganshi ka ga mai hannu da shuni. Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna ya kwalawa mai restaurant kira da karfi ya ce “Hado min plate na Naira 2,000 kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3, 000 saboda idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”. Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa ta kawo masa hadin girma. Shinkafa da dankalin turawa da farfesun kayan ciki ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so. Kana ga hadin kwadon kayan lambu da a turance a ke kira da salad Bayan mutumin ya gama cin abinci sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500 kuma ki baiwa kowa na Naira 1, 000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”. Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala. Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar “Allah ya kiyaye ka!” Bayan...
This blog is created to advertise products and enlighte people.